Enrolment options
A wannan mahajar karatun kai, zaka yi koyi ka kuma zama mai sanin fasahar zamani (Digital Enquirer): wanda zai bayyana yadda ake gano bayanan bogi a yanar gizo, hanyar samun labari, tattara labarin, yin nazarin bayanan da ake dogaro da su a yanar gizo, da kuma tura labaran ta amintacciyar hanya.
Wa ye zai iya amfana da wannan mahajar karatun? Masu amfani da fasahar zamani da keda muradin kyautata duniyar labarai da sadarwa. Ko da kuwa kai mai ra’ayin kare hakkin al’umma ne, dan kasa ko dan jarida. Ko kuma kawai kana bibiyar bayanai ne a yanar gizo, wannan darasin ya dace da kai!
Me zaka iya koya?
> Ganowa da magance bayanan bogi
> Tantance labarai da gane sahihancin su
> Aiki da sahihan bayanai da kiyayesu
> Sanin yadda zaka kare kanka ka kuma kare wasu
Tsawon wane lokaci kake bukata? Kowane sashi yana bukatar minti 15. A takaice dai, darasi guda zai shafe minti 90.
Wane takadar shaida zaka karba? Takardar shaidar kamala kowane darasi yayin da aka gama.
Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit (GIZ) GmbH ta haɓaka wannan sashin karatun tare da haɗin gwiwar Tactical Tech.
Lasisi: Creative Commons Attribution-Share A like 4.0 International (CCBY-SA4.0), Tactical Tech da GIZ.